By Abbas Yakubu Yaura
Makiyaya a ranar Laraba sun kori wasu al’umomi masu gonakin a kauyuka guda biyar a yankin Mgbuji mai cin gashin kansa, Eha-Amufu,dake karamar hukumar Isi-Uzo ta jihar Enugu, inda suka kashe mutane biyar da suka hada da yara da mata.
Wannan dai ya zo ne kwanaki biyar da kashe ‘yan kungiyar Unguwar Jihar guda uku a yayin da suke bin masu garkuwa da mutane domin ceto matar da diyar Dokta Eugene Edeoga ‘yar shekara 11, kanin Kwamishinan Muhalli na Jihar Enugu, Chijioke Edeoga, da aka yi garkuwa da su a ranar 1 ga watan Janairu, 2022.
Wakilinmu wanda ya ziyarci al’ummar Mgbuji a ranar Laraba, ya ruwaito cewa an ga mutane dauke da kayansu a guje suna kutsawa cikin garin daga matsugunan da ke fama da rikicin.
A gidan Cif Eric Ebe, daya daga cikin masu ruwa da tsaki a garin, yace an ga mata da yara sama da 50 da suka kubuta sun tsere daga matsugunan gonakin da ake fama da rikici a harabar.
Ebe a zantawarsa da wakilinmu, ya bayyana mamayewar da aka yi wa al’ummarsa a matsayin abin tsoro da rashin sanin yakamata.
Ya ce tun daga ranar 1 ga watan Janairu, an kashe mutane akalla 10 a yankinsa yayin da wasu da dama kuma aka yi garkuwa da su domin neman kudin fansa.
Wani shugaban al’ummar yankin, Cif Moses Olinya, ya koka da cewa sama da sa’o’i 24 da sanar da jami’an tsaro farmakin da aka yi na kashe-kashe, har yanzu ba su ga jami’an tsaro ba.
A cewarsa, wadanda ake zargin sun mamaye al’ummar ne da misalin karfe 10 na safe.
Wasu matan da suka rasa matsugunansu, wadanda suka zanta da wakilinmu, sun roki gwamnati da ta kawo musu dauki.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Daniel Ndukwe ta wayar tarho, bai amsa kiran da akayi masa ba.
Har ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, bai mayar da martani ga sakon da aka aike masa ba.
A halin da ake ciki, shugaban karamar hukumar Isi-Uzo, Jacob Abonyi, ya tabbatar da kai farmakin, inda ya bayyana hare-haren da ake kai wa al’ummar Mgbuji a matsayin abin da bai dace ba.
Abonyi ya ce, “Lokacin da na samu labarin a ranar Talata, na tuntubi ‘yan sanda amma lambar wayar jami’in ‘yan sandan shiyya a kashe, nan take na kira sojoji.
“Kusan kwanaki biyar da suka gabata, muna fama da garkuwa da mutane a cikin Mgbuji, lokacin da aka yi garkuwa da matar da diyar Eugene Edeoga kuma aka sake su ranar Litinin.
“Don haka, na kira sojoji kuma mun shirya a safiyar yau, ciki har da masu gadin unguwanni da masu gadin daji. Sai dai abin takaicin shi ne, sojojin da ke Ikem sun ce sun samu kiran gaggawa daga Uzo-Uwani kuma suka yanke shawarar komawa baya ba su dawo ba.