A safiyar Talatar nan ne mazauna garin Yantumaki dake karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina suka shiga zanga-zanga don nuna rashin jin dadinsu da irin yadda ‘yan ta’adda suka addabi yankinsu, amma ya zuwa yanzu babu wata rawa da gwamnati ta taka wajen basu agaji.
Wani wanda ya ganewa idonsa, ya shaidawa manema labarai cewa mazauna yankin sun fito mazansu da matansu; ciki har da matasa da kuma yara duk don su nuna rashin jin dadinsu.
Ya kara da cewa sun tare babban titin Katsina zuwa Kankara da manyan duwatsu da sauran abubuwan tare hanya, sannan sun kona tayoyi akan titi, wasu kuma na dauke da ganyayyaki wanda yake nuni da bacin ransu a fili.