A ranar Laraba ne mazauna unguwar Aerodrome da ke karamar hukumar Samonda a Ibadan suka gudanar da zanga-zangar lumana kan aikin gina masana’antar iskar gas a unguwarsu.
Kamfanin iskar gas din yana raba iyaka tare da gidajen mazauna yankin.
Mazauna yankin sun ba da misali da barazana ga tsaron rayuka da dukiyoyin su, inda suka bayyana wurin da aka gina masana’antar a matsayin rashin dacewa.
Kakakin su, Dayo Afolabi, ya ce, al’umar yankin sun dauki matakai daban-daban kafin a fara aikin, kuma sun yi kokarin ganin sun Gana da ma’aikatar albarkatun man fetur (DPR), da kuma masu saka hannun jari a kamfanin gas din, amma duk kokarin na su ya ci tura.
Ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su shiga tsakani tare da dakatar da ayyukan da ake yi domin hana afkuwar bala’i a jihar.
Sai dai jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, ba ta samu ji daga bangaren Hukumar DPR reshen jihar Oyo ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoto