Mazauna jihar Kaduna sun yi watsi da umarnin Gwamna Nasir El-Rufai na cewa su ci gaba da amfani da tsohuwar Naira 500 da Naira 1,000 a matsayin takardar kudi don yin mu’amala ta kasuwancinsu.
Malam El-Rufai, a yayin da yake gabatar da wani jawabi ga ‘yan jihar, ya bayyana manufar sake fasalin naira a matsayin makami da ‘yan jam’iyya mai mulki da makusantan shugaba Buhari suka yi niyyar amfani da shi domin yakar dan takarar shugaban kasa na APC Bola Tinubu, daga lashe zaben 25 ga Fabrairu.
KU KARANTA: Kyakkyawar Makomar Najeriya Na Tare Da Dan Takarar Shugaban Kasa Da Nake Ra’ayi – Wike
Wani direban bas, Mohammed Sani, ya shaida wa DAILY POST cewa, “Ba zan iya karban tsofaffin takardun kudi na N500 da Naira 1,000 daga hannun fasinjoji ba saboda ba zan iya amfani da kudin daya bani ba wajen siyen man fetur.”
Ya kara da cewa, “Idan kun je kasuwa, ba za ku iya amfani da tsofaffin takardun kudi don siyan komai ba, haka kuma ba za ku karbi tsohon takardun daga hannun kowa ba saboda ba za ku iya amfani da su wajen yin kasuwanci ba.”
Wani dan kasuwa a babbar kasuwar Kaduna, Alhaji Sale Musa, ya ce ba zai iya siyar da komai ba saboda yawancin mutane ba su da kudin.
“Ba wanda ya yarda ya yi amfani da tsofaffin takardun kudi ko karban duk wata ciniki ta kasuwanci.”
Ya ce ba za a yaudare shi da umarnin El-Rufai ba, wanda ta cikin shirin kai tsaye ga al’ummar jihar, ya umarce su da su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun Naira wajen gudanar da harkokinsu na kasuwanci.
Wani ma’aikacin banki, George Stephen, ya bayyana cewa ba su da izinin karbar tsofaffin takardun kudi na Naira 500 da kuma N1,000 daga hannun kwastomomi.
DAILY POST ta lura ana amfani da tsohuwar takardar kudi ta N200 kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarta, yayin da jama’a suka ki karban tsofaffin takardun N500 da N1,000.
A wani labarin kuma: Da Yiwuwar Ma’aikatan Bankuna Su Tsuduma Yajin Aiki a Ranar Litinin
Kalubalen samun sabbin takardun kudi na naira ka iya kara tabarbarewa daga ranar litinin inda ma’aikatan bankuna suka fara yajin aiki.
Wannan mataki na masana’antu, kamar yadda jaridar The Nation ta gano, ya biyo bayan harin da masu ajiyar tsofaffin takardun kudi na N,1000, N500 da N200 suka kai wa ma’aikatan bankuna.