Majalissar Dunkin duniya ta ce akalla fararan hula 136 ne suka Mutu tun bayan mamayar da Rasha tayi a Ukraine daga ranar Alhamis din data gabata zuwa yau
Kana 13 daga cikin wadanda suka mutu kananan yarane da harin na Rasha ya rutsa dasu.
Amma Liz Throssell, Mai magana da Yawun shugaban sashin kula da kare hakkin Dan Adam na majalissar ya ce, yawan wadanda suka Mutum ka iya karuwa a kowani lokaci.
Throssel ya ce, Akasarin gawarwakin mace-macen sun farune sakamakon makamai masu linzami, da harin jiragen Yakin da kuma fashewar Bama-bamai.
Kazalika Majalisar Dunkin Duniyar ta ce, mutane akalla 400 ne suka Sami mummunan raunuka sanadiyar harin.
A gefe guda alkaluman da Gwamnatin Ukraine ta fitar ya nuna cewa, Fararan Hula 352 ne suka rasa rayukan su, yayin da 1,684 suka Sami raunuka.