Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da kazamin harin ta’addancin da ya hallaka sojin kasar Mali kusan 30 a Mondoro dake tsakiyar kasar.
Wakilin Sakatare Janar na Majalisar na musamman akan aikin zaman lafiyar dake gudana a Mali, ya gabatar da sakon ta’aziyar Majalisar ga gwamnatin rikon kwaryar Mali da kuma jama’ar kasar tare da iyalan sojin da suka rasa rayukan su.
Wakilin ya dada jaddada aniyar rundunar MINUSMA ta Majalisar wajen tabbatar da zaman lafiya a cikin kasar ta Mali.
Rundunar sojin Mali tace sojoji 27 suka mutu, yayin da wasu 33 suka samu raunuka sakamakon harin Yan ta’addan.