Wasu daga ake zargin suna cikin membobin kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra (IPOB) a ranar Litinin sun hargitsa hukumar jarabawar WAEC a makarantar Sakandaren Nkume dake karamar hukumar Njaba ta jihar.
Wani Bidiyon da ya yadu a kafafen sada zumunta ya nuna yadda aka kori ɗalibai da masu sa ido daga zauren jarabawar kafin su cinna wa rufin ɗakin wuta.
IPOB ta dage kan umarnin ta na zama gida-gida a ranar Litinin a Imo duk da muhimman jarabawar harshen Ingilishi da aka shirya a wannan ranar.
Bidiyon ya kuma nuna yadda aka kona wasu babura da ake zargin na wasu dalibai ne yayin gudanar da harin.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda (PPRO) a Imo, CSP Mike Abattam, ya shaida wa NAN cewa har yanzu‘ yan sandan na duba faifan bidiyon don gano gaskiyar lamarin kafin fitar da wata sanarwa.