Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Lionel Messi ya zargi kungiyarsa da gaza lashe kofin gasar La Liga ta bana, inda ya ce dole ne salon buga tamola din su ya sauya, idan aka yi duba da yadda suke ci gaba da rasa maki a wasanni masu muhimmanci ciki har da rashin nasararsu a gida a hannun Osasuna, wanda hakan ya sanya babbar abokiyar hamayyarsu, Real Madrid ta lallasa Villareal wanda hakan ya ba ta damar lashe kofin na La Liga karo na 34 a tarihi.
Messi ya bayyana hakan ne a yayin zantawarsa da wata jaridar wasanni a Sipaniya, inda ya kara da cewa; ba ‘yan wasan kadai ke bukatar sauya salon taka ledarsu ba, har ma da shugabancin Barcelona baki daya wanda ke bukatar sauyi.
Babbar damar da ta ragewa Barcelona a yanzu bai wuce hada karfinta a wasannin gasar zakarun Turai da ke gabanta ba, duk da cewa gasar Zakarun Turai din da Copa del Rey sun zama babban kalubale ga kungiyar la’akari da yadda ya kasa kai kofunansu gida tsawon shekaru.
Akwai dai masu hasashen cewa rashin nasarar Barcelonar a yanzu na da nasaba da yadda kungiyar ta tattara Dattijan ‘yan wasan galibinsu ‘yan fiye da shekaru 30.