Bayanai na nuni da cewa kwararren dan wasan kwallon kafarnan, Lionel Messi ya kara kafa tarihi a karawar da Barcelona ta yi da Real Sociedad a daren ranar Lahadi, wanda hakan ya sanya shi ya zama a jiya ya buga wasanni 768 a Barcelona kawai.
Buga wannan adadin ya sanya ya yi daidai da Xavi Hernandez. An wallafa bidiyo da yawa a shafukan sada zumunta bayan Messi ya daidaita tarihin, ya ci kwallaye biyu kuma ya taimaka an ci daya a kan Huesca.
A wasan Real Sociedad, wanda shi ne wasa na 511 a gasar La Liga, yana neman neman maki uku don taimakawa kungiyar ta Barcelona neman lashe gasar La Liga Santander. Haka nan za su buga wasan karshe na Copa del Rey da Athletic Club a watan Afrilu.