Tsohon dan wasan baya na Barcelona Dani Alves ya yi imanin cewa Lionel Messi yana buga kwallo mafi takaici tare da cewa ya zama shi ne dan wasa da ke ceton kungiyar.
Alves ya ce Messi mutum ne da yake son tashi cikin nasara, kuma ba ya kaunar rashin nasara, “idan ya samu rashin nasara ran shi yana matukar damuwa. Yana son yin nasara kowane lokaci, kamar Ni.” Inji shi.
Alves ya bayyana hakan ne a yayin hira da gidan Talabijin na Cataluniya. Alves ya kara da cewa; Messi ya dade yana bautawa kungiyar Barcelona, “babu dan wasan da zai iya baiwa kungiyar nasarar da yake bata.” Inji shi.