Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain, Lionel Messi ya tabbatar da cewa zai koma Barcelona a nan gaba idan ya kammala wasansa.
Messi, wanda ya bar kungiyar ta Catalonia zuwa PSG a bazarar 2021, ya bayyana Barcelona a matsayin gidansa.
KU KARANTA: Ba Wasu Dattawa a Arewa, Mu Gwamnonin Arewa Mune Dattawan – El-Rufai
Ana kallon dan wasan mai shekaru 35 a matsayin daya daga cikin manyan ‘yan wasan kwallon kafa na Barcelona a kowane lokaci.
Da yake magana da Olé (ta Albiceleste Talk), gwarzon da wasan wanda ya lashe gasar cin kofin duniya na Argentina ya ce, “Idan na gama aikina, zan dawo da zama a Barcelona, domin gidana ne.”
Messi ya shafe shekaru 17 a tarihinsa mai ban sha’awa daga 2004 zuwa 2021 a Barcelona.
Ya kuma lashe kyautar Ballon d’Or sau bakwai ya lashe kyautar azurfa da yawa tare da Blaugrana, ciki har da UEFA Champions League da La Liga, da sauransu.
A wani labarin kuma; Ni Ina Kallon Peter Obi Kamar Jarumin Nollywood Ba Dan Takara Ba – El-Rufai
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Elrufai y ace dan takarar shugaban kasa na jamiyyar Labour Party Mr Peter Obi ba zai iya taba lashe zaben 2023 ba, balle burinsa na son zama shugaban kasa ya tabbata.
Malam Elrufai ya ce Peter Obi bashi da yawan magoya bayan da ake bukata dan takara ya samu balle a dinga la’akari da shi cikin sahun yan takara, hakan ya sanya yake kallon sa kamar wani jarumi a masanaantar fina finaI ta Nollywood.