
Wasan zai zama mafi zafi kasancewar kasashen ‘yan adawan junane tunda dadewa, Kuma zai iya kasancewa wasa mafi dadin kallo a gaba dayan wasannin.
Tarihi ya nuna cewa tun bayan haduwa kasashen biyu a wasan kusa da na karshen a shekarar 2016 inda faransa ta lallasa jamani daci biyu da nema, sannan da wasan karshen na zakarun turai tsakanin Bayern da PSG a shekarar 2020 wasannin ne Wanda aka baiwa hammata iska sosai.
A ranar Talatan nanne kasashen zasu sake karawa, inda jama’a da dama suke baiwa faransa damar lashe wasan duba da irin manyan ”yan wasan da ta tara., Duk da cewar itama abokiyar karawan ba daganan ba.
A wannan lokacin faransa nada damar sake nuna bajintarta kamar yadda ta nuna a kasar RUSSIA a shekarar 2018.
Gob Marcotti. Yace jamani itace kungiya mafi wahalar tunkara a duk nahiyar turai duba da yanayin ”yan wasan da ta hada. Amman duk da hakan zai basu mamaki.
KU KARANTA:-
China ta gargadi G7 cewa kada wani ya yi gigiwar hanata jujjuya duniya yadda take so
Ya Kara da cewa jamani nada harzikan ‘yan wasa irinsu Jushua Kimmich da Sane da sauran manyan ‘yan wasa masu hadari.
Sannan Mai jagorantar yan wasan Low yace dole ne suga sunyi nasara a wasan duba da irin rashin nasara da suka samu a wasanu da ya gabata kada a maimaita.
KUNA IYA KARANTA WANNAN:-
Dubu Sittin aka bamu mu kashe wani mutum: in ji wasu mutane a Kebbi
Jami’an rundunar tsaro ta Civil Defense a Jihar Kebbi sun yi nasarar chafke mutane biyu da aka yi hayarsu su lashe wani mutume dai an yi kwangilar su da aniyar hallaka wani mutum mai suna Gari Mamman mazaunin kauyen Lahore dake karamar hukumar Zuru ta Jihar ta Kebbi.
Kwamandan rundunar ta Civil Defense Alhaji Suleiman Ibrahim Marafa ya ce bisa bayanai da suka samu a gurin wadanda ake zargin, wani mutum ne mai suna Alhaji Mamman ya yi hayarsu da zummar wancan aika-aika, inda ya basu fashin alkalami naira dubu sittin cikin dubu tamanin da aka yi yarjejeniya.
Ya ce mutanen biyu masu suna Mando da Manu, sun banka wa gidan Gari Mamman amma daga bisani sun fahimci cewa ba ya gida.
Sai dai a wata tattaunawa da manema labarai, wanda ya bada kwangilar kisar ya musanta zargin, inda ya ce shi dai tura su ya yi su koya mishi hankali ba wai kashe shi ba.
Ya ce kuma dalilin shi na haka shine, yana zarginsa ne da hallaka mishi mahaifi watanni uku da suka wuce