Wani magidanci ya bayyana hotunan tsiraicin matarsa da babban abokinsa a shafukan sada zumunta bayan da ya kama su a tare.
Rahotanni sun nuna cewa; dama mijin yana zargin matar ta sa, zargin na shi bai tabbata ba har sai da ya kama matarshi da babban abokinsa tsirara a dakin abokin na shi.
Mijin ya rika lura da yadda matar ta shi ta kai wa abokinsa ziyara a dakinsa, inda watarana ya kai wa abokin na shi ziyarar bazata da yammaci. Dama can abokin na shi makwabcinsa ne.
Sai dai da mamakinsa, kwatsam ya ga abokin na shi da matarsa tsirara sun saduwa da juna sun kuma manta ba su kulle kofa ba.
Duk da yanayin da ya gansu, bai dauki matakin duka ba, amma sai ya dauki hoto da su ya nuna wa duniya.