Rundunar ‘yan Sandan jihar Ogun ta garkame wani mutum mai suna Kingsley Madukwe mai shekara 40 a duniya bisa zargin dukan matarsa mai suna Gloria, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarta. Wanda ake zargi din dan garin Ihiala ne, a jihar Anambra.
An kama shi sakamakon rahoton da wani mai suna Rafiu Gbadamosi daga Baale a Egando dake Atan-Ota, a karamar hukumar Ado Odo/Ota ya shigar.
Bayanai sun nuna cewa; ma’auratan sun samu sa6ani ne, inda mjjin ya jibgi matar har rai ya yi halinsa. Kakakin ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya kara da cewa; DPO na Atan Ota, SP Salau Abiodun shi ya jagoranci zuwa wurin, inda aka kama wanda ake zargi.
Oyeyemi ya ce a yayin binciken wanda ake zargi, ya ce ya mari matarsa ne a yayin da ta ki bai wa jaririnsu nono ya sha.