Mijina Da Shettima Su suka fi dacewa su Mulki Najeriya – Oluremi Tinubu
Uwargidan dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki kuma Sanata mai wakiltar Legas ta tsakiya, Oluremi Tinubu, ta ce tikitin hadin gwiwar mijinta, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da Sanata Kashim Shettima, ya ba da kyakkyawan fata na wakilci da kuma tabbatar karfafawa matan Najeriya.
Ta bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja a wajen taron tattaunawa na zaben mata da kungiyar Asiwaju Women Cooperative Society (AWCS) ta shirya a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ambaliyar Ruwa: Mutane 18, 406 ne suka rasa muhallansu a Borno
Sanata Tinubu ta samu wakilcin tawagar mata ‘yan siyasa a wajen taron da suka hada da Hon. Tolulope Akande-Sadipe, Hon. Olubunmi Ogunola, Hon. Adewunmi Onanuga, Zainab Gamawa da Rinsola Abiola.
A jawabin Hon. Tolulope Akande-Sadipe, Tinubu ya ce ba za a iya cin zabe ba tare da goyon bayan mata ba.
A wani labarin kuma: Ambaliyar Ruwa: Mutane 18, 406 ne suka rasa muhallansu a Borno
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno, SEMA, ta ce akalla mutane 18,406 ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a kananan hukumomi 14 na jihar.
Darakta Janar na Hukumar Yabawa Kolo ce ta bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a Maiduguri ranar Litinin.