Babban Antoni janar na kasa Abubakar Malami SAN ya ce, Matakin Mika dakataccen Mataimakin Kwamishinan Yan sanda Abba Kyari zuwa kasar Amurika, Kutu ce kawai za ta iya yanke hukunci kan lamarin.
Ya kara da cewa, da yuwuwar a bi dukkannin ka’idujin da Kotun Amurika ta Gindaya kan Wannan batu.
Malami ya bayyana hakan ne, a jiya Alhamis lokacin da ya ke zanta wa da kafar yada labarai ta VOA, Inda ya yi nuni da cewa, duk da cewar akwai yarjejeniyar Mika mai laifi tsakanin Nigeria da Amurika, amma akwai wasu ka’idoji da ya kamata abi.
Ya ce ” Hakika akwai yarjejeniyar tsakanin Nigeria da Amurika kan mika duk wanda ya aikata laifi a kasashen biyu, Ko a Nigeria ko a Amurika, Amma akwai ka’idojin rubuta wasika ga Ma’aikatar kula da harkokin kasashen waje, Sanna Ma’aikatar ta aike da sokon zuwa Antoni janar, kafin daga bisani ya amince da Mika koma waye, domin ya je kasar ya amsa wasu tambayoyin kan zargin da ake masa” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mayakan Boko Haram da ISWAP 56 sun Mika wuya
Kazalika ya kuma ce, Kowa ce kasa cikin kasashen biyu, za ta iya bukatar hakan, domin amince wa da Mika wani idan ya aikata mummunan laifi.
“Bance za a Mika Abba Kyari ba, Amma zamu bi ka’idojin doka kafin mu dauki mataki” inji shi.
Sai dai tuni aka yi wa Abba kyari wani daurin talala na tsawon kwanaki goma kamar yadda wata Kotu dake Yankin California na karsar ta bukata.