Majalisar wakilan tarayya ta umarci kwamitin ta kan harkokin albarkatun man fetur da ya gudanar bincike don gano gaskiyar yadda kudin gyaran mamatatar mai na Fatakwal wanda gwamnatin tarayya ta amince da shi.
baya ga wannan kuma majalisar ta umarci kwamitin da ya bankado yadda aka samo kudaden gyaran matatar man na Fatakwal da ma sauran matatun mai a fadin kasar nan.
Wannan mataki da majalisar ta dauka ya biyo bayan wani kudiri ne da ya shafi jama’a wanda wani dan majalisa mai suna Onofik Luke ya shiagar gaban majalisar.
Yan Majalisaar sun ce gwamnati ta kashe kudade masu dimbin yawa wajen gudanr inganta matatun man to amma kawo yanzu babu abinda ya sauya zani.
Idan za a iya tunawa dai a makon da ya gabata ne hukumar Zattaswar tarayya ta amince da dala miliyan daya da rabi a matsayin kudin aikin matatar man na Fatakwal wanda ta ce nan take za a fara aikin.
Karamin Ministan Man Fetur Timipre Sylva wanda ya bayyana haka jim kadan bayan wata ganawa da Hukumar zattaswar ta gudanar ya ce aikin matatar man za a yi shi mataki-mataki har guda uku.
Sylva ya ce rukuni na farko za a gudanr da shi ne cikin watannni goma sha takwas sai rukuni na biyu cikin watanni ashirin da hudu yayin da rukuni na uku kuma na kasrhe za a yi ne cikin watanni arba’in da hudu.