Minista ta yanke jiki ta fadi a Bauchi
Maryam Katagun Ministan Kanfanoni da habbaka kasuwanci, an ruwaito ta Fadi kasa a wajan taro a Bauchi a ranar Litini.
Katagun wadda ta halarci wani taron gaddamar da tallafi na habbaka noma da kasuwanci (NAAADI) a Shopping Plazas a Bauchi.
KARANTA:-Matsalar Tsaro: Gwamnatin jihar Kaduna ta rufe Makarantu 13
Shaidar gani da ido, yace ta yanke jiki ta fadi a lokacin da take gabatar da bayani.
Ministan bayan ta dan dau lokaci tana bayani tazo karshen wajan rufewa sai ta fara layi zata fadi nan take na kusa da ita suka tallafa mata kamin ta kai kasa. Kamar yadda shaidar gani da ido ya bayyana.
Nan take Akai gaggawar kaita Asibitin Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi don kulawa.
Kawo yanzu dai babu wani bayani daga mahukunta da suka fitar, amma wani daga ciki ma’aikata ya bayyanawa Channel Tv tana cikin yanayi mai kyau a lokacin da ake dauka rahotan.
Kamar yadda wani ya bayyana, yace Katagun ya bayyana rashin gamsashshiyar lafiyar ta kamin ta fara gabatar da bayani.
Taron ya sami halartar gwamna Baba Tela na Jahar Bauchi.