Hajiya Sadiya Umar Farouq, ministan jin kai ta mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan da suka rasa ‘ya’yansu guda shida a jihar Zamfara.
Rahotanni sun bayyana cewa yaran shida sun rasa ransu ne a lokacin da suka shiga daji nemo itatuwa a kauyen Magami dake karamar hukumar Maradun a jihar, inda suka yi arba da wadannan abubuwa masu fashewa, ya fashe da a yayin da suke wasa da shi.
Farouq a wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba a Abuja, wanda mai taimaka mata kan harkokin lura da kafafen watsa labarai, Nneka Anibeze ta sanyawa hannu, ta bayyana mutuwar yaran a matsayin abu mai kada zuciya. Sannan ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da suna kiyaye irin wadannan abubuwa masu fashewa domin gudun fadawa hannun da bai dace ba.