Karamin Ministan Kwadago da nagarta ayyuka, Festus Keyamo, ya yi kira ga iyayen da yajin aikin malaman jami’o’i ya rutsa da ƴaƴansu kan su yi kira ga kungiyar Malaman Jami’o’i da ta dakatar da yajin aiki da take.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, ASUU ta fara yajin aiki a fadin kasarnan, a ranar Litinin, 14 ga Fabrairu, 2022.
Yajin aikin a cewar kungiyar ya biyo bayan gazawar gwamnati wajen biyan wasu bukatu da suka hada da sakin kudaden farfado da jami’o’i, sakin alawus-alawus da sauran su.
DUBA WANNAN LABARIN: Isra’ila ta farmaki Gaza, yayin da itama ta mayar da martani
Tun bayan fara yajin aikin, masu ruwa da tsaki sun yi kira ga gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da ta samar da mafita ga malaman don su kawo karshen yajin aikin.
Shugaban kasar, a wata ganawa da ya yi da Ministan Ilimi, Adamu Adamu, tare da sauran takwarorinsa, ya bayar da umarni ga ‘yan majalisar ministocinsa da abin ya shafa, da su tabbatar an gaggauta magance matsalar yajin aikin.
Sai dai kusan makonni uku da umarnin shugaban kasa, kungiyar ta kasa dakatar da yajin aikin da take yi.
Da yake gabatar da shirin a gidan Talabijin na Channels, Keyamo ya bayyana cewa gwamnati ta yi iya bakin kokarinta, ya kuma yi kira ga iyaye da su “roƙi kungiyar ASUU.”
Yanzu abun jira dai a gani shine zuwa yaushe kungiyar zata janye yajin aikin, duba da cewa yau kusan watanni 6 ke nan tana gudanar da shi.