Rahotannin da ke shigo mana na tabbatar da cewa; ministan harkokin wajen Nijeriya, Geoffrey Onyeama ya kamu da cutar annobar korona.
Ministan ya tabbatar da hakan ne a shafinsa na Twitter, inda ya ce an tabbatar masa da cewa ya kamu da cutar bayan an yi masa gwajin cutar a karo na hudu.
A cikin sakon da ya wallafa, ministan ya kara da cewa; “a yanzu haka ya kama hanyarsa ta zuwa wurin killace masu ɗauke da cutar.” Inji shi.