Daga: Abbas Yakubu Yaura
Ministan Ilimi, Adamu Adamu, a ranar Litinin din da ta gabata, ya yi kira da a yi adalci a daidai lokacin da aka fara daukar dalibai a makarantun Unity mallakar gwamnatin tarayya na shekarar 2022/2023.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta ruwaito cewa hukumar shirya jarabawar ta kasa ta sanar da fitar da jarabawar gama gari ta shekarar 2022 a watan Yuni.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/%c6%b4an-daba-sun-jikkata-mambobin-pdp-suna-tsaka-da-taro-a-kogi/
Duk da cewa Adamu bai bayyana matakin kayyade adadin makin kowace jiha ba, amma ya bukaci shugabannin makarantun Unity ta kasa da su rungumi ka’idojin daidaito da adalci.
Sanarwar da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi Ben Goong ya fitar a wani bangare na cewa, “Yayin da shugabannin kwalejojin Unity ta kasa guda 110 suka hallara a birnin Benin, babban birnin jihar Edo domin fara karbar tallafin ilimi na bana. Ministan, Adamu Adamu, ya ba da umarnin cewa dole ne a yi musu jagora bisa ka’idojin adalci, daidaito da kuma sanin yakamata wajen gudanar da daukar dalibai.”
A sakon da ta gabatar a wajen bude taron a madadin ministar, Darakta a manyan makarantun sakandire, Binta Abdulkadir ta ce, “Idan har za mu samar da ‘yan kasa masu hazaka, dole ne mu tsaya a kan ka’ida don yin zabin da ya dace na kwararru. ‘yan takara a matsayin tushe don samu ƙwakkwaran ilimi a nan gaba.”
Ministan ya tunatar da shugabannin makarantun cewa su tsaya kan tsarin kasa na rabon malami daya zuwa dalibai 40 a aji daya bisa ka’idojin UNESCO, ya kara da cewa dole ne a bi tsarin daukar nauyin karatun.
Adamu ya jaddada cewa “ya kamata a baiwa ‘yan takarar da suka nemi shiga makarantun Unity da ke wajen yankunansu.”
Ministan ya umurci shugabannin makarantun “su bi ka’idojin zabe wanda ya dace da kashi 60% na a matakin kasa, kashi 30% na jihohi da kuma kashi 10% na ficewa.”