Kungiyar Likitoci masu neman Kwarewa ta Najeriya ta dora alhakin shiga yajin aikin kan Ministan Kwadago da ayyuka chris Ngige da kuma Ministan Lafiya Dakta Osagie Ehanire, musamman kan matsayar gwamnati.
Idan za a iya tunawa a ranar biyu ga watan Afirelun 2021 Ngige ya ce gwamnatin tarayya za ta ayyana tsarin nan na “Ba aiki, ba albashi” muddin suka ki fita aiki.
Ya ce tun ba yau ba gwamnati ta cika wa kunigiyar duk bukatun ta amma ya rasa wace tsiyar ce ta hana su komawa bakin aiki duk irin namijin kokarin da gwamnatin tarayyar.
Likitocin sun bukaci gwamnatin da ta gaggauta biyan su albashin da suke bin ta da sauran bukatun ta daban daban.
a yake tattaunawa da tashar talabijin ta Channels shugaban Kungiyar Uyilawa Okhuaihesuyi ya ce dole ne gwamnatin ta biya musu bukatunsu indai har tana so su koma bakin aiki.
Uyilawa ya ce gwmantin ta gaza tsayawa a alkibla guda ce kawai amma cikin bukatu bakwai da ta gabatar mata dakyar ta biya ma kungiyar guda daya.