Wasan hamayya na El Classico wasa ne da ake fafata shi tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid wadda take a babban birnin Andalus da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona wadda take a yankin Catalonia na ƙasar ta Andalus kuma wasa ne da ake ganin babu kamarsa wajen hamayya a duniya.
Wasan dai wasa ne da hamayyarsa ta ɗakko asali tun lokacin siyasa a shekaru aru-aru da suka gabata inda koda ba ta fannin wasan ƙwallon ƙafa ba hamayya ce mai zafi tsakanin muyanen da suke zaune a yankin Catalonia da kuma mutanen da suke zaune a yankin Madrid.
Hakan ce ma tasa har yanzu wasu mazauna birnin na Catalonia suke furtawa da kuma iƙirarin cewar zasu fita daga yankin na Andalus domin waremusu tasu ƙasar mai suna Catalonia inda har yanzu suna tayar da rigima akan hakan.
A ranar 24 ga watan Oktoba ne dai na shekarar nan ta 2020 za a fafata wasan na hamayya tsakanin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan guda biyu wato Barcelona da Real Madrid, inda za a fara fafata wasan farko a birnin Catalonia wato a filin wasa na Camp Nou wato wasan mako na 7 kenan.
Sai dai dangane da wannan wasa ministan lafiya na birnin Catalonia yayi magana musamman danbane da shigar ‘yan kallo su kalli wannan wasa na hamayya, inda yace baza a bar ‘yan kallo ba su shiga domin kallon wannan wasa duba da cewar har yanzu cutar nan ta Coronavirus tana ci gaba da rugurguzar mutane a nahiyar ta turai.
Idan za a iya tunawa dai ita ƙasar Andalus tana daga cikin ƙasashen da wannan cuta ta yiwa ɓarna sosai da sosai, ganin hakan yasa aka yanke hukuncin cewar ‘yan kallo sam bazasu sami damar shiga kallon wasan ba na El Classico tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona da Real Madrid.
A wannan rana ta Asabar Real Madrid zata fafata da Cadiz a filin wasa na Alfredo de Stefano yayin da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona zata kaiwa Getafe ziyara, ita dai Barcelona tana da kwantayen wasanni guda biyu yayin da ita kuma Real Madrid tana da kwantan wasa guda ɗaya. Haka zalika Real Madrid ce take jan ragamar teburin da maki 10 daga cikin wasanni 4 data fafata.