Ministan shari’a na ƙasa Abubakar Malami, ya ƙi bayyana gaban kwamitin tsohon shugaban kotun ɗaukaka ƙara, Ayo Salami, dake binciken dakataccen shugaban hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziki ta’annati (EFCC), Ibrahim Magu.
Mai shari’a Salami, ya gayyaci Malami ne domin bayar da shaida kan takardar zargin da ya rubuta wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, da ta haifar da naɗa kwamitin da ke bincikar Magu.
Gayyatar ta biyo bayan roƙon da Magu ya yi wa kwamitin na a bashi damar fuskantar waɗanda suke zarginsa, ciki har da ministan shari’ar.
https://dimokuradiyya.com.ng/an-saki-tsohon-shugaban-efcc-ibrahim-magu/
A cewar takardar gayyatar, “Ana baka umarni da sunan shugaban ƙasar Najeriya, ka bayyana gaban kwamitin bincike na shari’a domin bayar da shaida kan zargin da ka ke yiwa Ibrahim Magu”.
Maimakon ya bayyana, sai Malami ya rubuto wa kwamitin cewa ba zai bayyana a matsayin shaida ba, saboda takardar da ya rubuta na ɗauke ne da zarge-zargen wasu suka kawo masa ne akan Magu.
Idan ba a manta ba, Ministan shari’a, a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise ya sha alwashin amsa kiran kwamitin binciken a matsayinsa na Malami ko kuma ministan shari’a .