Ministan Shari’a na tarayya Najeriya Abubakar Malami ya janye daga takarar gwamnan jihar Kebbi, domin ya gaji Atiku Bagudu wato gwamnan jihar mai ci yanzu haka.
Wannan na zuwa ne watanni bayan da Ministan Shari’ar ya shiga cikin sahun masu neman takarar Gwamnan Jihar Kebbi, wanda kuma ya samu tarin magoya baya.
Da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Birnin Kebbi, Malami ya godewa daukacin magoya baya da suka bashi gudunmawa wajen nuna masa soyayya da kuma goyon baya.
Jin kadan bayan kammala taron sai Ministan ya gwangwaje wasu daga cikin wadanda suka bashi gudunmawa kyautar motoci na alfarma domin saka musu, kuma da yawan su masu riƙe da gidauniyar Ministan ce.
Malami ma daga cikin ministocin da shugaba Buhari ya yi sallama da su tare da fatan alkhairi, bayan da suka ajiye Mukaman su wasu kuma ke shirin ajiyewa, amma daga bisani sai ya fice daga cikin yan takarar domin ci gaba da kasancewa a minista.
Umar Jibrila Gwandu shine mai magana da yawun Ministan kuma da aka tuntube shi, ya ce baida cikakkiyar masaniya kan wannan batu, amma dai ya sani cewa Shugaban kasa ya baiwa masu riƙe da Mukaman siyasa umarnin ajiye mukaminsu domin shiga zaben 2023.