Karamar ministar babban birnin tarayya, Abuja. Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu, ta fuskanci Suka a lokacin da ake gabatar da takardun shaida ga zababbun shugabannin kananan hukumomin burnin a yau Juma’a.
Kwamishinan zabe na jihar Alhaji Yahaya Bello ne ya mika takardar shaidar a wani biki da ya samu halartar manyan ‘yan siyasa.
Yayin da ministar take jawabi wasu daga cikin magoya baya sun Fara ihu, da kuma nuna rashin amincewa da Kalaman Ministar, cewa ya Kamata Hukumar zabe ta Samar da wata hanya da Al’umma zasu iya zabe ta tsohuwar hanya baya ga ta zamanin da ake tafiya akai.
An samu korafe korafe Kan hukumar INEC a yayin zaben kansiloli da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.
Duk da hakan Amma suka fara ihu suna cewa, ‘Karya ne ba ma so’, ma’ana “Karya ce, ba ma so”.
Ministar ta yi ƙoƙari ta kwantar da hankulan jama’ar da suka ji haushi amma suka yi mata ihu da sautin “Ba ma so”.
Sanata Philip Aduda, wakilin babban birnin tarayya Abuja a majalisar dokokin kasar ya fusata ya fice daga wurin taron. Yayin da Jami’an tsaro a wurin taron suka kasa shawo kan ‘yan jam’iyyar.