Primate, da ke cocin kasar nan, Anglican Communion, Most Rev. Henry Ndukuba, ya bayyana fatansa na cewa kasar za ta shawo kan kalubalen da take fuskanta, ta kuma kara karfi a tsakanin kasashen duniya.
Da yake jawabi a sakonsa na Kirsimeti a cocin Cathedral Church of Advent, Life Camp, a Abuja, Archbishop Ndukuba ya ce haihuwar Yesu Kiristi ya sanya bege ga dan Adam.
Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da kada su ji tsoron kalubalen amma su dubi Allah da ya yi alkawarin fitar da kasar nan daga halin da take ciki da kuma ‘yantar da ‘yan kasar.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa, Primate ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi imani da Allah kada su ji tsoro domin nufin Allah ga Najeriya zai zo nan ba da dadewa ba.
KARANTA KUMA Kirsimeti Ta Kawowa ‘Yan Najeriya Kwanciyar Hankali
A cewarsa, akwai fata ga Najeriya yayin da al’ummar kasar ke ratsawa a kan abin da suke ratsawa a daidaiku, a matsayin iyali, a matsayin jama’a, da kasa baki daya.
“A irin wannan lokacin, kamar yadda yake a Kirsimeti na farko, sa’ad da aka haifi Yesu, saƙon Mala’ika ga makiyayan, waɗanda suke kamar mutanen da aka yi watsi da su, waɗanda ake zalunta kuma ba a kula da su a cikin al’umma.
“Lokacin da Allah ya so ya ba da labarin haihuwar Yesu, su ne mutane na farko da Allah ya faɗa abin da sama ya yi, wato, Allah yana daraja kowa.
“Allah yana kula da mutane, musamman wadanda aka zalunta, wadanda ke cikin wahala, da wadanda ba su da mutunci, ba su da daraja.”
Primate ya yi kira ga kiristoci da su zama mutane na gari don abubuwan da za su yi aiki a kansu. (NAN)
A Wani Labarin Kuma Gwamna Ya Caccaki Tsohon Gwamna Saraki, Da Ahmed Akan Wasu Kudaden UBEC
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara a ranar Lahadi ya caccaki tsohon shugaban majalisar dattawa, Dakta Bukola Saraki da ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP a jihar kan zargin almubazzaranci da kudaden hukumar ilimin bai daya (UBEC).
Gwamnan, a yayin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben dan takarar kujerar Sanata na jam’iyyar APC a jihar Kwara ta tsakiya, Malam Saliu Mustapha a Ilorin, musamman ya zargi tsohon Gwamna Abdulfattah Ahmed da saka hannun jari a fannin ilimin firamare.