Kungiyar Miyetti Allah ta MACBAN reshen jahar Yobe ta bukaci gwamnatin jihar da ta kaddamar da shirin RUGA wanda gwamnatin tarayya ta samar.
Sakataren kungiyar, Bello M. Bello ne ya fitar a ranar Laraba inda ya ce kaddamar da shirin za ta karawa makiyaya ingancin rayuwa. Ya kara da cewa shirin za taimakawa wajen habbaka tattalin arzikin makiyaya da ma jihar ta hanyar samun karuwa shanu da madara tare da naman sa
Ya jaddada cewa shirin yana da matukar amfani ga ci gaban jihar musamman wajen kawo karshen rikice-rikice da kungiyoyi daban-daban ke fuskanta da juna a jihar.