Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Hore ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su tabbatar an shigar da sauran kabilun kasar musamman ma Fulani cikin duk wani shiri da za a yi na samar da tsaro a yankin Kudu maso Yammacin kasar. Kamar yadda BBC Hausa suka tabbatar.
Kungiyar na yin wannan kira ne bayan cimma matsayar da aka yi tsakanin gwamnonin yankin da ma’aikatar shari’a kan cewa jihohin na Kudu maso Yamma su bi tsarin da doka ta tanada wurin kirkirar kungiyar Amotekun.
Ita dai kungiyar ta Kautal Hore ta nemi a soke kungiyar ta Amotekun, wadda za ta samar da tsaro a jihohin Yarabawa.
Shugaban kungiyar ta Miyetti Allah Kautal Hore a Najeriya, Alhaji Bello Abdullahi Bodejo ya ce a hangensu kungiyar “ba za ta yi wa Fulani adalci ba da sunan samar da tsaro”.