By Abbas Yakubu Yaura
hamshakin attajirin dan kasar Sudan da Birtaniya kuma shugaban gidauniyar Mo Ibrahim Mohammed Ibrahim ya yi Allah wadai da juyin mulkin da aka yi a Sudan a ranar Litinin.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa A ranar Litinin din da ta gabata ne babban Janar din Sudan ya ayyana dokar ta baci, bayan ya rusa shugabannin rikon dimokradiyyar kasar, tare da sanar da kafa sabuwar gwamnati.
Bayan haka ne sojoji suka tsare fararen hula da suka hada da Fura Minista da wasu jami’ai.
A cikin wata sanarwa da gidauniyar Mo Ibrahim ta fitar a baya-bayan nan ta yi Allah wadai da juyin mulkin tare da yin kira ga sauran abokai da kawayen Sudan da su yi hakan.
Sanarwar ta bayyana cewa Mo Ibrahim yayi kira ga, “gwamnatin kasar Sudan da ta mika mulki ga dimokuradiyya, wanda al’ummar Sudan suka yi kokarin tabbatar da tsaro, na fuskantar hare-hare ne biyo bayan kwace madafun iko.
“Gidauniyar tana nuna cikakken goyon bayanta ga Firayim Minista Abdalla Hamdok da tsarin mika mulkin sa.
“Ina kira ga kawayen Sudan na duniya da su tofa albarkacin bakinsu a yanzu domin yin Allah wadai da abin da ake cewa juyin mulki, da kuma daukar dukkan matakan da suka dace don ganin cewa ci gaban da aka samu cikin shekaru biyu da suka gabata bai tafi a banza ba.