Mohamed Salah ya ci gaba da nuna bajintar sa a Liverpool bayan da ya zura kwallaye biyu a wasan da suka doke Atletico Madrid da ci 3-2 kuma ta dare saman rukunin B a gasar zakarun Turai.
Atletico ta yi rashin nasarar da ‘yan wasa goma a fili, bayan da aka kori Antoine Griezman a mintuna na 52 sakamakon yadda ya daga kafa fiye da kima har zuwa fuskar dan wasan Liverpool Roberto Firmino, bayan kwallaye biyu da ya zura a ragar Liverpool.
Sauran wasannin rukuni-rukuni na gasar Zakarun Turai da aka fafata ranar Talata.
Rukunin A
Bayaga wasan PSG da RB leipzig
Club Brugge -1 Manchester City- 5
A rukunin B
Bayaga wasan Liverpool da Atletico Madrid
Fc Porto -1 Ac Milan- 0
A rukunin C
Besiktas -1 Sporting CP – 4
Ajax -4 Borussia Dortmund- 0
A rukunin D
Bayaga wasan Real da Shaktar Donetsk
Inter -3 Sheriff -1