Mohamed Salah, kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Masar kuma fitaccen dan wasan Liverpool, ya bayar da gudunmawar kudi domin sake gina cocin Abu Sefein da ke gundumar Giza, bayan wata gagarumar gobara da ta yi barna a makon jiya.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Kafofin yada labaran kasar sun ce Salah ya ba da gudummawar dalar Amurka dubu 156,000 (kimanin fam miliyan 3 na Masar) don sake gina cocin.
Jirgin Abuja-Kaduna: Sauran Da Suka Rage Suna Cikin Wani Hali —- Mai Shiga Tsakani
A ranar Lahadin da ta gabata ne wata gobara ta tashi a cocin Abu Sefein inda ta kashe mutane 41 tare da jikkata akalla 14.
Salah ya jajanta wa wadanda suka mutu a cocin ta shafinsa na Twitter, sa’o’i kadan bayan faruwar lamarin.
Salah ya rubuta: “Ina mika ta’aziyyata ga wadanda suka mutu a Cocin Abu Sefein, tare da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.”
Shafin yanar gizo na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ya nuna alhini ga wadanda gobarar cocin ta shafa a Masar.
Liverpool ta bayyana a shafinta na Twitter cewa, “Ta’aziyyarmu daga Liverpool FC zuwa ga dukkan iyalan wadanda suka mutu a gobarar Cocin Shahida Abu Sefein a gundumar Giza, Masar, muna fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.”
Hukumar kwallon kafa ta Masar ta mika ta’aziyya ga wadanda gobarar cocin Giza ta shafa.
Masu jimamin lamarin a Masar sun halarci taron tunawa da wadanda gobarar Coptic ta shafa a ranar Talata – daga cikinsu akwai yara da dama da suka hada da tagwaye da ‘yan uku.
Gobarar da wutar lantarki ta haddasa ta tashi a ranar Lahadin da ta gabata, inda ta mamaye cocin Abu Sefein da ke Imbaba, wata gunduma a yammacin kogin Nilu, wanda kuma ya kasance wani yanki na gundumar Giza a babban birnin Alkahira.