Wata mota cike da Matafiya ta faɗa a wani ƙaton rami a yankin Oworonshoki dake Jahar Lagos.
A cewar rahoton, wasu daga cikin matafiya sunji raunuka a lokacin wannan lamari daya faru a ranar Litinin.
An kuma gano cewa, motar ƙwacewa tayi, kafin ta faɗa ƙaton ramin da har yanzu ba’a san ko matafiya nawa ne.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jami’ar Abia Ta Kori Wani Malami Biyo Bayan Badakalar Yin Lalata Da Daliba Don Bata Maki
A cewar Jaridar PUNCH ana ƙoƙari domin ganin an ceto matafiyan da lamarin ya rutsa dasu.
Babu wani cikakken rahoto har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.