By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa an tabbatar da mutuwar wata mata da yaronta da kuma mutum daya a wani mummunan hatsarin da ya afku a tsohuwar hanyar Legas zuwa Asaba, Boji-Boji Owa, a karamar hukumar Ika ta Arewa maso Gabas a jihar Delta.
Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro cewa, bala’in ya afku ne a lokacin da wata tankar mai dauke da man fetu ta samu matsalar birki, inda ta kutsa cikin motoci da masu tafiya a kasa da dama a kan hanyar.
Rahotanni sun bayyana cewa mutanen uku da suka mutu sun rabe daga jikinsu a hatsarin.
Wani ganau ya shaidawa wakilinmu cewa hatsarin ya afku ne da misalin karfe 5 na yammacin ranar Litinin, 24 ga watan Janairu, 2022, daura da mahadar Okoh.
“Matar marigayiyar tana kan babur din ta, inda ta nufi hanyar mahadar da ‘ya’yanta uku da ta dauko daga makaranta a lokacin da motar ta kutsa cikin su tayi awon gaba da su.
“Matar, danta da kuma wani mutum guda sun mutu nan take. Wasu da suka hada da babban yaron marigayiyar an ce sun samu raunuka daban-daban kuma an garzaya da su babban asibitin Agbor domin kula da lafiyarsu,” inji ganau ya kara da cewa.
Tawagar hadin gwiwar sojojin Najeriya da hukumar kiyaye hadurra ta tarayya da kuma ‘yan sanda daga Owa-Oyibu da kuma bangaren Agbor ne suka yi tattaki zuwa wajen da shugaban karamar hukumar Ika ta Arewa masu Gabas, Victor Ebonka.
Shugaban karamar hukumar, wanda ke wajen da hatsarin ya afku har aka kawo wata kora mai dauke da tankar, ya hana matasan da suka fusata kona tankar mai dauke da man fetur.
Ya jajanta wa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, inda ya bayyana hatsarin a matsayin abin tausayi da takaici, domin ya bukaci matasan da kada su dauki doka a hannunsu.
“Tankar cike take da man fetur kuma idan har kuka yi kokarin kunna mata wuta, to a zahiri kun kunna kan ku ne domin ko shakka babu wutar da ke fitowa daga mai zai cinye ku.
“Mun samu nasarar ceto daya daga cikin yaran tare da mika ta ga mahaifinta, yayin da wasu da ke cikin motocin da aka murkushe a kan layi aka kai su wani asibiti da ke kusa. An sanar da ni cewa suna karbar magani,” a cewar Ebonka.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, ba a san inda direban tankar ya ke ba.