Wata motar sintiri ta hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) a jihar Bauchi ta kashe mutane biyu tare da raunata wasu biyar bayan ta kutsa kai cikin wani shago dake wurin ajeyi Motoci na Alkaleri dake kan babban hanyar Bauchi zuwa Gombe.
Kwamandan hukumar FRSC na Gombe, Yusuf Abdullahi ne ya tabbatar wa manema labarai afkuwar hatsarin ranar Lahadin da ta gabata a Bauchi.
Mista Abdullahi ya bayyana cewa: “Ma’aikatanmu suna dawowa sansanin ne yayin wani sintiri na yau da kullun. Nan take direban ya yi ihu ya kashe wutar. Haka ya motar takwace ya bar hanya gaba daya.
“Motar sintiri ta kutsa kai cikin wasu mutane da ke tsaye kusa da wani shago a yankin. Ya tsaya lokacin da ya bugi shagon. Wasu mutanen da ke cikin shagon ma sun samu raunuka. Mutane 14, da suka kunshi manya 10 da yara hudu ne lamarin ya rutsa da su.
“Kalubalen lafiya na iya faruwa ga kowa kuma a kowane lokaci. Har yanzu direban ba ya hayyacinsa a babban asibitin Alkaleri,” inji shi.
Ya roki iyalan wadanda abin ya shafa, inda ya ce, “A madadin hukumar, zukatanmu na kai gaisuwa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu. Muna kuma yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki. An ajiye gawarwakin a dakin ajiyar gawa yayin da wadanda suka jikkata ke karbar magani a asibiti daya” a cewar shi.