By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane biyu ne suka mutu tare da jikkata wasu mutane biyun a wani hatsarin mota daya afku a ranar Talata a babban birnin tarayya Abuja.
An bayyana cewa hatsarin ya afku ne da misalin karfe tara na safe a yankin dajin Idu dake babban birnin tarayya Abuja.
Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro cewa hatsarin ya afku ne lokacin da wata motar dakon siminti ta kutsa kan wasu matuka babur mai kafa uku guda biyu da kuma mota guda daya.
An ce mutane biyu sun mutu nan take, yayin da wasu biyu da suka jikkata aka garzaya da su zuwa asibitin Crown dake Gwagwa.
Wani mazaunin garin, Johnson Oye, ya ce, “Shi (direban babbar mota) ya zo ne domin samar da siminti ga wadanda ke gina gidaje a nan. Ba za mu iya cewa ko da gaske ya rasa iko ko yana ƙoƙari ya riske su ba, sai kawai muka ga motar ta kutsa kan babur guda biyu da motar guda daya.
“Matukin babur din ya samu mummunan rauni kuma an kai shi Asibitin Crown, Sauran biyun da suka mutu suna daya daga cikin babur din mai kafa uku. Direban motar bai tsaya ba bayan ya buge su, a shirye ya ke ya murkushe duk wanda ya tsaya a kan hanyarsa.”
Daya daga cikin wadanda suka tsira, wacce ta bayyana sunanta Alimat, ta ce za ta kai wa yaron ta da bai da lafiya magani a lokacin da hadarin ya rutsa da ita.
Ta ce, “Mai tuka babur din da na hau ya samu munanan raunuka.”
Kwamandan sashin kiyaye hadurra na babban birnin tarayya Abuja, Samuel Ochi, ya ce bai san da faruwar hatsarin ba.