By Abbas Yakubu Yaura
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ekiti, Tunde Mobayo, a ranar Laraba ya tabbatar da cewa wani mataimakin Sufeto na ‘yan sanda ya gamu da hatsarin yayin da motar sintiri ta tureshi akan babur din sa wanda ta kashe shi har lahira yayin da wasu ‘yan sanda takwas suka samu raunuka a wata tawagar jami’an tsaro ta Ado Ekiti.
Mobayo, wanda ya nuna alhinin rasuwar dan sandan tare da tausaya wa wadanda suka jikkata, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa motar ‘yan sandan ta murkushe dan sandan daya mutu har lahira a yayin da suke bin wasu da ake zargi da damfara ta yanar gizo wato Intanet.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, CP, Sunday Abutu, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon lankwasa da motar ‘yan sandan ta yi, yayin da jami’an RRS ke kan hanyarsu ta zuwa amsa kiran gaggawa da aka yi musu.
Yace, “da misalin karfe 6:30 na yamma, DPO, Ikole Ekiti, jami’an RRS suka yi kira da a karfafa musu gwiwa domin kamo wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne, wadanda suka addabi al’ummar Ikole-Ekiti da kewaye.
“Bayan samun rahoton, Kwamandan RRS ya tura motocin sintiri guda uku tare da isassun jami’ai a yankin domin gudanar da aikin simamen.
“Abin takaici, a yayin da suke kan hanyarsu, daya daga cikin motocin ‘yan sintiri uku ya samu matsala, inda ya fita daga layinsa, ya bugi wani babur da ke tafe da wani dan sanda, wanda ya tashi daga aiki yana kokarin komawa gida.
“An garzaya da dan sandan asibiti domin kula da lafiyarsa, amma likita ya tabbatar da mutuwarsa, yayin da wasu jami’an RRS takwas da ke cikin motar sintiri suka samu raunuka daban-daban kuma a halin yanzu suna asibiti ana kula da lafiyarsu.”
Abutu ya bayyana cewa Mobayo ya tausaya wa iyalan dan sandan da ya rasu tare da yi masa addu’ar Allah ya ba shi hutu na har abada.
A cewar PPRO, CP ya ziyarci ‘yan sandan da suka jikkata a asibiti sannan kuma zai ziyarci iyalan marigayin ASP.