Guda daga cikin masu zanga-zanga a Sudan ya rasa ransa bayan wata Babbar Mota ta bi ta kansa a ranar Alhamis yayin da suke Tattaki.
Mai shekara 23n Wanda ke daya daga cikin masu nuna adawa da gwamnatin mulkin sojin kasar a Khartoum na daya daga cikin masu zanga-zangar dake Tattaki zuwa fadar gwamnatin Sudan, kamar yadda kwamitin likitoci kasar suka wallafa a shafinsu na Tiwita.
Al’uma da dama a Sudan na cigaba da zanga-zangar kin Jinin Juyin Mulki da Sojoji suka yi tun a watan Octoban bara, inda gwamman mutane suka rasa rayukansu yayin arangaman da jami’an tsaron kasar.
Mutuwar matashi na nuna cewa, kawo yanzu adadin masu zanga-zangar da suka mutu ya Kai 95 a cewar Kwamitin likitoci.
A wani labari Kuma na daban
Yayin da ake ci gaba da tsare jagoran ‘yan asalin yankin Biafra, Nnamdi Kanu da kuma yunƙurin neman shugabancin ƙasar Igbo a 2023, shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Ohanaeze Ndígbo da shugabannin yankin kudu maso gabas a jihar Ebonyi.
Wakilan Kudu-maso-Gabas da suka gana da Buhari a ranar Juma’a a sabon dakin taro na exco Chambers,a gidan gwamnati dake Abakaliki sun samu jagorancin shugaban kungiyar Ohanaeze, George Obiozor,
Ko da yake ba a iya samun cikakken bayanin taron ba, Ohanaeze a wata sanarwa daya fitar ranar Talata a karshen taronta da aka gudanar a Abakaliki, ta ce ziyarar aiki ta kwanaki biyu da Buhari zai kai Ebonyi, za ta fara aiwatar da shirin ne domin a samu saukin sakin Kanu tare da matsa kaimi wajen ganin an sako Kanu Shugaban ‘yan kabilar Igbo a Najeriya.
Sanarwar ta kara da cewa, “Ohanaeze Ndigbo Worldwide ta bayar da tabbacin zaman lafiya da tsaro gabanin ziyarar da shugaban kasa zai kai jihar Ebonyi….Amma fatan Ndigbo shine a yi amfani da irin wannan tagomashin don samun sakamako mai kyau domin shugaba Buhari zai samu nasara da Ndigbo.
Wannan zai kasance daya daga cikin manyan ziyarar da mai girma shugaban kasa zai kai yankin Kudu maso Gabas, domin muna sa ran ziyarar aiki ta kwanaki biyu da shugaban kasa zai yi a jihar Ebonyi za ta sauya labarin cewa Buhari na son Ndigbo, kuma zai tabbatar da hakan ta hanyar kaddamar da yakin neman zabe. tsarin da zai saki Nnamdi Kanu.”
“Ya kamata kungiyar IPOB da sauran masu fafutukar kafa kasar Biafra su ci gaba da zaman lafiya kuma su kasance masu biyayya ga tsarin da zai taimaka musu wajen ganin an sako shugabansu, Mazi Nnamdi Kanu.
Ziyarar ta Buhari za ta haifar da sabon fata na samun shugaban Najeriya na ‘yan kabilar Igbo da kuma tabbatar da sakin Mazi Nnamdi Kanu.”