‘Yan Shi’a Almajiran Shaikh Ibrahim Zakzaky, sun gudanar da Zanga-zangar Lumana a garin Abuja, ta neman a Saki Jagoransu a Yau Laraba, inda suka fara daga Banex Plaza da ke Wuse II, wacce sukai ma take da Karyar Ku Munafukai ta Allah ba taku ba, Free Zakzaky Dole.
Wakilin Jaridar Dimokuradiyya, ya samu Zantawa da Jagoran taron Malam Sunusi Abdulkadeer, Wanda ya ce Babu ruwanmu da masu cewa wai mun dakatar da yin zanga-zanga zuwa wani lokaci, domin mu Addini muke yi ba Siyasa ba.
In baku Manta ba a dazu ne Wata Sanarwa ta Fito wacce ta karade Kafafen Yada labarai Daban-daban cewa ‘yan Shi’a sun dakatar da yin zanga-zanga zuwa wani lokaci, Shehin Malamin Ya ce mu Mabiya Malam Ba mu dage yin Zanga-zangar lumana ba, domin ko yau ma mun yi kamar yadda kake gani yanzu.
Malam Sunusi, ya cigaba da cewa Muddin Kaji wani yana cewa shi mabiyin Malam Zakzaky ne kuma amma yake cewa a dakatar da yin Zanga-zangar lumana wacce muka shafe sama da shekaru muna gudanar wa to lallai wasu yake ma aiki ya sani ko bai sani ba, illa iyaka.
Dan haka muna kira da babban murya duk wani mabiyin Malam Zakzaky na gaskiya to ya zo Abuja, domin Bada tashi gummawa wajen sauke hakkin jagora da yake kan sa, inji shi.