Malamai a Jami’ar Prince Abubakar Audu a ranar Laraba sun bayyana cewa bazasu je yajin aikin gargaɗi da Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta ayyana.
Shugaban Tsangayar Ilmi ta Jami’ar Farfesa Ogunbiyi Joseph ya bayyana haka a tattaunawar sa da Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa a Anyigba na Kogi.
Mr Joseph yace Jami’ar bata daga cikin yajin aikin gargaɗi na ASUU da aka fara a ranar Talata.
“A matsayin mu na Malaman Jami’ar Prince Abubakar Audu, bama daga cikin yajin aikin ASUU, kuma bazamu iya binsu ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Chidinma Osuji A Matsayin Babbar Darakta Ta NDIC
“Abu na biyu ya saɓawa ƙa’idojin Jami’ar da Gwamnan Kogi Dr Yahaya Bello, amma wani abun farin ciki ga Gwamna shine, duk abinda Gwamnatin Tarayya ta amincewa ASUU, bayan fadan su, to shi (Yahaya Bello) yana zartar dashi a garemu ba tare da mun shiga anyi yaƙin damu ba.
“Bari in sanar daku cewa, abunda muke samu a nan Jami’ar, shine dalilan da suka sanya babu tsaiko ga jadawalin karatun mu,” inji shi.
Shugaban Tsangayar yace a lokacin taron yaye Ɗalibai karo na 6 a Jami’ar, Gwamna Yahaya Bello ya baiwa jami’ar gashin kanta akan dukkanin kuɗaɗen da ta samu, a matsayin wani ƙudiri kyakkyawa ga Jami’ar.