Kungiyar masu fafutukar ganin sun kafa kasar Biafra, wato IPOB, ta gargadi tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso.
A cewar kungiyar su suna naɗi ne, ba wai zabe ba, a don haka Kwankwaso ya kiyayi kansa, daga danganta ya’yan kungiyar da zaben gama gari da za ayi a Najeriya.
Kungiyar ta kuma gargadi yan siyasar Najeriya, da ma shi kwankwason kan sa da su guji alakanta kungiyar su da Peter Obi.
Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Peter Obi shine ɗan takarar shugaban a jam’iyyar LP, kuma ya fito ne daga yankin da yan IPOB din suka fi kaurin suna.
To sai dai IPOB ta ce duk da kasancewar Peter dan yankin su ne, amma hakan bai bashi damar zama san cikin kungiyar su ba, kuma ba nasu bane.
Wata Sanarwa da suka gabata ga manema labarai ta hannun jami’in hulda da jama’ar na kungiyar, Emma Powerful, sun ce tsarin da Peter Obi kwata kwata bai dace da irin tsarin kungiyar su ba.