Kungiyar mata ta kasa, NCWS, a ranar Juma’a ta yi kira ga ‘yan Nijeriya akan su ci gaba da addu’o’i domin ganin an samu zaman lafiya, hadin kai da walwala a fadin kasarnan.
Laraba Shoda, shugaban kungiyar ta NCWS ce ta bayyana hakan a sakon da ta aike na sabuwar shekara a ranar Juma’a a Abuja.
Shoda ta ce ya zama wajibi a daidai wannan lokaci a rika maganganu da za su samar da zaman lafiya da hadin kai idan aka yi duba da kalubalen da kasarnan take fuskanta na matsalar tsaro da kuma annobar cutar Korona.
“a yayin da muke shiga 2021, muna amfani da wannan damar wajen ganin an yi addu’o’in zaman lafiya a kasarnan”. Ta lurantar.