Gwaman jahar kebbi Abubakar Atiku Bagudu, yayi wanann magana a ranar asabar yayi kira kan Al’ummar kasa kan tallafawa Gwamnatin tarayya wajen magance matsalar tsaro a fadin kasar nan.
Inda yace ta haka ne za a sauke nauyi da ya rayata kan shugaban ni dama mutanen kasa.
Yayin da yake wannan magana yace annoba ce babba ta faru a kasa musamman arewacin Najeriya yakin namu ne baki daya inji shi.
A matsayin sa na babban bako a gun taron da ministan yada labarai da al’adu Lai Muhammad ranar 12 a karamar hukumar irepodun ta jahar Kwara.
Ya kara da cewa mu daina nuna ban bancin kabila ko al’ada mu Daura damar yaki da wanann dabia ta matsalar tsaro a fadin kasar nan a cewar Bagudu.