Fitaccen Fasto din nan na jihar Kaduna, wato Fasto Yohana Buru ya yi Allah-wadai a tir da sace wadansu Yara ‘yan asalin jihar Kano da wadansu Inyamurai suka yi, suka siyar da su a jihar Anambra tare da sauya musu addini.
Ga Bayanin da Fasto din ya wallafa a shafinsa na Facebook.
MU KIRISTAN NIJERIYA, MUN YI ALLAH WADAI DA SATAR YARA TARA A JIHAR KANO!
Muna gan tabbacin satar Yaranmu tara watau maza da mata da aka kaisu jihar Anambra, watau kudu masau gabas. Wannan abin Allah wadarne! Har ma muna gani da kuma karantawa akan cewa wadansu yaran an mayar dasu Kirista.
To abin yi na farko shine, muna neman gafaran iyayen yaran, Al’ ummah Musulmi, Kanawa, ‘Yan Arewa da Nijeriya gaba daya.
In kuma sun mayar da su Kirista, to ba haka ake shigar da mutum cikin addinin Kiristanci ba. Domin sai mutum ya gane da menene addinin Kirista kafin ya karbi addinin Kirista ko furuta Kalmar Shahadah Romans 10:9-10.
Ba a Satan mutum a shigar dashi a addinin Kirista, ba tilasta mutum ya shiga addinin Kirista, ba a yaudaran mutum ya shiga addinin Kirista ko abi wata hanya da mutum baya cikin hankalinsa, ko halin matsi da ire-irensu.
Sun cutar da yaran ne kawai kuma basu yi nasara ba, domin sun bi hanyan da ba dai ba. Sun sami dama na raba yaran da iyayensu amma na kankani lokaci ne kawai, amma basu cimma burinsu ba!
Domin da haka a matsayina na Kirista da kuma mallamin addinin Kirista da sauran Kiristan Nijeriya mun yi tir da Allah wadar da Wannan abin kunyan da suka yi. Don Allah muna rokon gafara daga iyaye, Kanawa, Musulmai, ‘Yan Arewa da Nijeriya gaba daya.
Ayi hakuri! Amma ayi masu hukunci daidai da laifinsu.