Muddin Aka yi Sahihin ZaɓeAPC za ta sha Kaye – Wike ya mayar wa Buhari martani
Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya bayyana cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Zata yi rashin nasara, idan har Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya dage wajen ganin an gudanar da sahihin zabe a 2023.
Wike ya ce APC za ta yi rashin nasara a 2023 idan Buhari ya dage a yi zabe mai inganci.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Ni ba mai Biyayya bace ga Peter Obi, Amma zanyi mashi aiki yaci Zaɓe- Aisha Yesufu
Da yake jawabi a wajen kaddamar da aikin gina titunan cikin gida na Igwuruta a karamar hukumar Ikwerre ta jihar, Wike ya godewa shugaban kasar bisa alkawarin ba zai yi katsalandan a zaben 2023 ba.
A cewar Wike: “Na gode wa shugaban kasa saboda yana son barin gudanar da sahihin zabe a Najeriya.
“Na gode wa Allah mai girma shugaban kasa da ya ce ba za ya tsoma baki ko tsorata kowa ba. Hakan na nufin jam’iyyar ku ba ta da hanyar samun nasara.”
A ranar Talata, Buhari ya yi alkawarin tabbatar da kidaya kuri’un ‘yan Najeriya a 2023.
Ya ce za a bar ‘yan Najeriya su zabi shugabanninsu a matakai daban-daban a zabe mai zuwa.
Buhari ya ce ‘yan Najeriya za su yaba wa jam’iyyar APC nan da watanni shida masu zuwa.
A wani labarin kuma: Ku tafka Babban Kuskure – Kungiyar Musulunci ga Iyalan Harin Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna
Kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC) ta yi kira ga iyalan wadanda harin jirgin kasa ya rutsa da su a layin dogo na Abuja zuwa Kaduna da su bar aikin jirgin ya dawo.
MURIC ta yi wannan roko ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktanta, Farfesa Ishaq Akintola kuma ta mika wa manema labarai a safiyar ranar Juma’a.