A ranar Asabar fadar shugaban kasa, ta bayyana cewa Malam Mamman Daura, yana da dama ya bayyana ra’ayinsa, a don haka ra’ayinsa da ya bayyana akan mulkin karba-karba, ba da yawun shugaba Buhari ko gwamnatinsa ya yi ba.
Bayanin martanin ga Malam Mamman Daura, ya fito ne daga sanarwar da Kakakin shugaban kasa Malam Garba Shehu ya fitar a birnin tarayya Abuja.
Garba Shehu ya ce Malam Mamman Daura, a matsayinsa na Dattijo a kasa yana da damar ya bayyana ra’ayinsa kamar yadda dokokin kasa ya ba shi dama.
“Ba shi da bukatar wani ya ba shi umurni domin ya bayyana ‘yancinsa.” Inji shi.
Garba Shehu ya ce an nemi da fadar shugabar kasar ta yi sharhi ne akan jawabin da Malam Mamman Daura, ya yi a yayin zantawa da BBC Hausa kan ra’ayinsa akan mulkin karba-karba.
“yana da kyau a sani cewa, abin da wanda aka tattauna da shi (Malam Mamman Daura) ya bayyana ra’ayinsa ne kashin kansa, ba ra’ayi ne ta kowanne fuska da ya shafi gwamnatin shugaban kasa Buhari ba.” Inji shi.