An tabbatar da mutuwar mutane 10 tare da raba wasu da dama da muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa a karamar hukumar Girei da ke jihar Adamawa.
Girei yana kusa da Yola ta Arewa, da kuma Yola ta Kudu, ƙananan hukumomi uku ne dake cikin babban birnin jihar wato Yola.
Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Adamawa (ADSEMA), Dokta Suleiman Muhammad, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho da yammacin Juma’a.
Suleiman ya ce mutane 10 sun mutu tare da raba wasu da dama a garin Girei hedkwatar karamar hukumar Girei da Jabi Lamba, mahallin su.
Sakataren na ADSEMA ya ce an gano gawarwaki shida yayin da har yanzu ba a kai ga gano wasu hudu ba.
Ya kuma bayyana cewa ambaliyar ta kai ga kwantar da yara uku a asibiti bayan da wani gini ya rufta musu a Girei.
Ya ce tun daga lokacin ne hukumarsa ta tura tawagar da ta zuwa yankunan da abin ya shafa domin tantance abubuwan bukatun agaji, kuma zai tuntubi Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) domin ta shiga tsakani.
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa Yola ta samu ruwan sama na tsawon lokaci a ranar Alhamis, wanda aka fara daga karfe 11 na safe har zuwa misalin karfe 3 na rana.
Sai dai Rahotonni sun bayyyana cewa, Ba a samu rahoton ambaliya a cikin babban birnin Yola ba, da alama saboda ingantattun hanyoyin ruwa