Wata mai shekaru 30 Hauwa’u Adamu dake da juna biyu, tana saran samun cikakkiyar kulawar lafiya a yayinda ta shiga tsarin waɗanda za’a duba a Cibiyar kula da lafiya a matakin Farko ta Dogon Daji. Tana dai saran cewa zata samu taimako da kula, amma abun yaci tura.
Amma abun baƙin ciki, wannan cibiyar lafiya, tana da Malamar jinya guda ɗaya, wadda itama sanya kanta tayi, inda take duba fiye da mata 60 masu juna biyu a kowacce rana, wasu daga cikin matan suna zuwa ne daga Jahar Jigawa.
“Wasu lokuttan ganin wannan Malamar jinya ba tabbas bane cewa zai samar da magani akan cutar da mutum ke fama da’ita; zaka iya ganin ta, amma sai ka koma gida ba tare da karɓar magani ba,” Adamu ya shaidawa wakili.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jam’iyar APC Ta Gargadi Rochas Okorocha Da Ya Guji Bata Sunan Gwamna Hope Uzodimma
Da wuya idan akwai wani magani a cibiyar da ake baiwa marar sa lafiya idan zasu koma gida.
Umma Sani, ƴar shekaru 35, wadda ke fama da cutar hawan jini, ta bayyana cewa ta daɗe tana zuwa Babban Asibitin Ƙaramar Hukumar su na Baraya Amma kullum kalma ɗaya take ji “likita baya nan”, ko kuma suce ka dawo gobe, ko sati mai zuwa, kuma babu tabbacin ganin likitan a wannan lokacin.
A Binciken da cibiyar binciken ƙwaƙwaf na aikin jarida tayi, ya nuna cewa Likitan dake Akwai a Babban Asibitin Baraya shine Dr Mohammed Maaji, Wanda ganin sa kaɗai wani abun cigaba ne. Abun damuwar Umma shine duk ƙoƙarin ta na ganin Likita, abun ya ci tura.
A binciken da ICIR ta gudanar a Ƙaramar Hukumar Jama’are a Jahar Bauchi dake da yawan mutane dubu 176,075 a shekarar 2018, tana da likitoci guda biyu, da Malaman Jinya guda 21 dake aiki a Babban Asibitin su, sauran cibiyoyin kiwon lafiya guda 29 da Asibitin Kuɗi na yankin, dukkanin su babu ma’aikata masu yawa.
Ƙaramar Hukumar Bauchi idan muka duba, tana da cibiyoyin kiwon Lafiya 113, daga cikin su guda 105 dukkanin su na Gwamnati ne, sauran 8 kuma na ƴan Kasuwa. Akwai Likitoci 83 da aka rarraba a Asibitocin Gwamnati 105, wanda yawan mutanen su shine dubu 737,575, a cewar Hukumar Ƙididdigar Jama’a ta Ƙasa a rahoton ta na shekarar 2006.
Asibitoci guda biyu na Manyan Makarantu a Jahar, da suka haɗa da Asibitin Koyarwa na Abubakar Tafawa Ɓalewa, da Asibitin Ƙwararru na Jahar Bauchi, waɗanda suke kula da marar sa lafiya da yawan su yakai 20,700 zuwa 18,750, suna da likitoci 37 da 25 a kowanen su.
A Ƙaramar Hukumar Darazo, kilomita 100km daga Babban Birnin Jahar, likitoci guda biyu ne da suke aiki a ƙarƙashin Gwamnatin Jahar, da yawan mutane 375, 796, ƙaramar hukumar tana da cibiyoyin kiwon lafiya guda 61, da Malaman Jinya guda 16, da ɗakunan gwaje-gwaje guda 16 gami da malaman unguwar zoma guda 8, da Ma’aikatan lafiya na Al’umma guda 54.
Irin wannan mummunan hali haka yake a Ƙaramar Hukumar Gamawa, inda ake da likitoci guda biyu da Malaman jinya guda 17 kaɗai, dake aiki a Babban Asibiti dake da mutane dubu 427,761, dukkanin sauran cibiyoyin kula da lafiya guda 58 basu da likita koda guda ɗaya.
A Ƙaramar Hukumar Kirfi dake da yawan mutane 220,488, tana da cibiyoyin kiwon lafiya guda 39 da likitoci guda biyu, da Malaman Jinya guda 9.
Ko a binciken da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Tafawa Ɓalewa Likitoci guda biyu ne ke aiki a Babban Asibitin Boto da Tafawa Ɓalewa. Ƙaramar Hukumar nada yawan mutane 339,755. Dukkanin Asibitocin, suna da Malaman jinya guda 17.
A Ƙaramar Hukumar Alkaleri, inda Gwamnan Bala Mohammed ya fito, lamarin haka yake. Ƙaramar Hukumar nada Asibitoci 56, har da Babban Asibitin Alkaleri, yana da Likitoci guda biyu, Malaman Jinya 18, da Malaman Unguwar Zoma guda 17, da ɗakunan gwaje-gwaje guda 30, gami da Ma’aikatan kula da lafiyar Al’umma guda 72.
Rashin Ma’aikata a Asibitocin Jahar, wannan ne ya sanya wasu ke tafiya Jahohin dake Maƙwabtaka dasu kamar Filato da Jigawa suke tafiya domin neman lafiya.
Asibitoci a Jahar bawai kaɗai sun wargaje ba, amma har da rashin kayayyakin aiki, duk da kasafin kuɗi da tallafi daga Ƙungiyoyin Duniya dana cikin gida, amma har yanzu babu wani cigaba ba.
Wani Malamin jinya (an ɓoye sunan sa domin gudun korar sa) da yayi aiki a Babban Asibitin Warji na tsawon shekaru 5, ‘ba’a taɓa wani lokaci da gwamnati ta bada magunguna a Asibitin ba”.
Wani Malamin Jinya a Jahar ya shaidawa ICIR cewa “lamarin abun baƙin ciki ne, aiki yayi yawa a garemu, shiyasa wani lokacin mutum yana iya abinda ba dai-dai ba ga marar sa lafiya.”
ICIR ta zanta da Ma’aikatan Jinya guda 40 da Likitoci a faɗin Jahar, dukkanin su sun bayyana yadda aiki yayi yawa, ƙarancin kayayyakin aiki, rashin magani