Tsohon kwamishinan yada labarai da al’adu na gwamnatin tarayya, Manjo Janar Ibrahim Bata Malgwi Haruna (rtd) ya dora alhakin matsalolin da Najeriya ke fuskanta a kan jerin munanan shugabancin da aka yi mata tsawon shekaru.
Haruna, wanda ya kasance kwamishinan tarayya daga 1975 zuwa 1977, ya bayyana hakan ne a Ilorin, babban birnin jihar Kwara a ranar Asabar da ta gabata a wata zantawa da manema labarai a matsayin bako a gasar wasan kwallon golf da aka gudanar domin karrama Hon. Mai shari’a Mudashiru Oniyangi, wanda aka gudanar a gidan wasan Golf na Ilorin.
Da yake amsa tambaya kan halin da kasa ke ciki a karkashin tsarin dimokuradiyya da na soja, jigon yakin basasar ya ce Najeriya ba ta samu shugabanci nagari a karkashin mulkin soja ba kuma ba ta samu ba a lokacin mulkin dimokuradiyya.
Ya koka da irin mummunan halin da kasar nan ke ciki a halin yanzu, na matsalolin tsaro, da cin hanci da rashawa, yana mai bayyana hakan a matsayin “sakamakon gazawar da sojoji da shugabannin dimokuradiyya suka yi ne a kasar tun bayan samun ‘yancin kai.
“Shin mun sami dimokuradiyya ta gaskiya ko kuwa mun sami gwamnatin soja ta gaskiya? Ba zan iya sukar soja da dimokuradiyya ba sai dai gazawarsu ita ce ta kai mu inda muke a yau.
Yan Takarar Shugaban Kasa Na Yankin Kudu Maso Gabas Na Ganawar Sirri
“Da sun yi nasara, da ba za mu sami rashin tsaro a cikin kasa kamar yadda muke a yau ba, da ba mu da ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, da ba mu da jami’an gwamnati da suka hada baki wajen wawure Naira biliyan 80 a cikin kasafin kudi,” inji shi.
A cewarsa, “Abin da muke ci a yau shi ne hadakar nasarori da gazawar gwamnatocin da suka gabata amma tsoron da muke da shi a yau shi ne kada mu yi watsi da alheran da muka samu mu maye gurbinsa da mafi muni,” kamar yadda ya yi gargadin.
Haruna ya ce kasar za ta iya magance wasu matsalolin ta da taimakon ‘yan jarida da shugabannin cibiyoyi, inda ya ce, “ku dubi ASUU, za mu iya magance matsalarsu, kudin mu da hauhawar farashin kayayyaki ke cinyewa, amma ‘yan jarida da kuma yadda za mu iya magance matsalar su. shugabannin cibiyoyi duk suna fuskantar kalubale.”
Dattijon ya kuma lura cewa rashin tsaro a kasar na iya haifar da rashin tambas da ke kara ta’azzara a tsakanin ‘yan kasar, musamman talakawa da marasa galihu.
Ya ba da shawarar cewa kasar za ta iya fita daga cikin dimbin matsalolin da take fama da su ne ta hanyar gaskiya, jajircewa, kishin kasa da sauya tunani.
I.B.M Haruna, kamar yadda aka fi sanin shi a lokacin da yake Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na Tarayya, ya kafa Hukumar Gidan Talabijin ta Kasa (NTA) a shekarar 1975 da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), sannan kuma ya ba da shawarar kafa Majalisar ‘Yan Jarida ta Najeriya da dai sauransu.
Ya bar aikin sojan Najeriya a matsayin Manjo Janar a shekarar 1977.
Kana Kuma a wannan shekarar ne aka nada shi shugaban kungiyar ‘Nigerian Participation in Africa’s Festival of Arts and Culture (FESTAC’77).